Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta ce a shirye take ta koma fagen yaki idan Iran ta ki amincewa da yarjejeniya

Amurka ta ce a shirye take ta koma fagen yaki idan Iran ta ki amincewa da yarjejeniya Amurka ta ce a shirye take ta koma fagen yaki idan Iran ta ki amincewa da yarjejeniya
Pete Hegseth

Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa sojojin ƙasar sun shirya tsaf don sake komawa yaƙi idan Iran ta ƙi amincewa da yarjejeniya.

Ya ce duk da cewa Amurka na fifita bukatar warware rikicin ta hanyar sulhu, amma rundunonin sojinta suna cikin shiri na ɗaukar matakin soja cikin gaggawa idan tattaunawa ta gaza.

Hegseth ya kuma gargaɗi cewa rashin amincewa da yarjejeniyar na iya haifar daukar tsananin matakan soji, yayin da Amurka ke ci gaba da matsin lamba domin Iran ta amince da sharuɗɗan da ake tattaunawa a kai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use