Turkiyya ta bukaci Amurka da Iran su gudanar da tattaunawa cikin gaskiya domin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu.
Turkiyya ta bayyana cewa za ta ci gaba da goyon bayan tattaunawar zaman lafiya.
Ta ce tana hulɗa da ɓangarori daban-daban ciki har da Pakistan domin tabbatar da tsagaita wuta ya zama na dindindin.
A cewar ma’aikatar tsaron ƙasar, akwai buƙatar tsagaita wuta da za a yi ya koma cikakken zaman lafiya mai dorewa ba tare da sake fuskantar rikici ba.
Haka kuma, ana sa ran ministocin harkokin wajen Turkiyya da Pakistan da Saudi Arabia da Masar za su gana a Antalya domin tattauna hanyoyin samar da mafita ga rikicin.