Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani ga Atiku Abubakar kan kalamansa game da zaben 2027, inda ta ce dole ne Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga, ya bayyana cewa ya kamata a mutunta tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da kuma Kudu, yana mai cewa yanzu lokaci ne na yankin Kudu ya ci gaba da rike mulki.
Fadar shugaban Najeriyar ta kuma zargi Atiku da saba wa wannan tsarin a baya, tare da buƙatar ya daina tunanin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.