Israel ta sake kai hare-hare a wasu yankuna na Lebanon, duk da ci gaba da tattaunawar sulhu a Washington.
Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 13, yayin da wasu kuma suka jikkata.
Lamarin ya faru ne kasa da awanni 24 bayan ganawar jami’an diflomasiyya daga ɓangarorin biyu, lamarin da ke nuna tabarbarewar ƙoƙarin kawo zaman lafiya a yankin.