Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ana shirin mayar da tubabbun ‘yan ta’adda 700 cikin al’umma

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen mika ‘yan ta’adda 700 da suka tuba çıkın sauran al’umma.

Wannan na zuwa ne yayin da rundunar ta yi watsi da zargin cewa ana ɗaukar waɗanda ke cikin shirin Operation Safe Corridor domin shiga cikin rundunar soji.

Rahotanni sun ce mai kula da shirin, Brigadier Janar Yusuf Ali, ya bayyana haka ne yayin rangadi a cibiyar gyaran hali da sake tarbiyya da ke jihar Gombe.

Ya ce shirin na gwamnati yana da nufin dawo da zaman lafiya a yankunan da ta’addanci ya shafa, yana mai cewa mutane da dama ba su fahimci yadda shirin ke aiki ba.

An gudanar da rangadin ne a matsayin shiri na bikin yaye waɗanda aka gyara, inda aka cire mutum sama da 700 cikin tsattsauran ra’ayi kuma za su koma cikin al’ummar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use