Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi gargadi kan abin da ta kira ayyukan kama-karya na bogi da wasu masu kwaikwayo ke aiwatarwa a manyan biranen Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Dele Oyewale ya fitar a ranar Talata, hukumar ta ce wasu “mugayen mutane” na amfani da dabaru daban-daban domin bata sunanta.
Sanarwar ta ce akwai ‘yan damfara da ke fakewa a wuraren cin abinci da wuraren shakatawa, suna tare matasa da zargin su da zamba ta intanet ba tare da hujja ba, sannan su ƙwace musu kayansu masu daraja.
EFCC ta kuma ce wasu daga cikinsu na yin sojan gona a matsayin jami’an hukumar, inda suke tafiya da waɗanda suka kama zuwa wurare da suka yi kama da ofisoshin hukumar.
Yayin da wasu kuma ke tsayar da direbobi suna karbar kudade da makamai bisa zarge-zargen ƙarya.
Haka kuma, akwai masu ƙirƙirar bidiyoyin bogi a intanet da ke nuna kamar EFCC na kai samame, lamarin da ka iya ruɗar da jama’a su ɗauka cewa jami’an hukumar ne ke aikata waɗannan ayyuka.