Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
'Yan bindiga sun sace dalibai a hanyarsu ta zuwa rubuta jarabawar JAMB a Benue
Kotu ta bai wa EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai Sadiya Faruoq

Kotu ta bai wa EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai Sadiya Faruoq

Kotu ta bai wa EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai Sadiya Faruoq Kotu ta bai wa EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai Sadiya Faruoq
Sadiya Umar Faruq

Wata kotu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta bai wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin-ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq.

EFCC dai na binciken tsohuwar ministar da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma’aikatar da ake zargin an yi sama da fadi da shi.

Wani saƙo da EFCCn ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali.

Hukumar ta ce matakin ya zo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.

Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya da ya hana Sadiya Farouq halartar kotun, sai dai kotun ba ta amince da buƙatar tasu ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use