‘Yan bindiga sun sace fasinjoji 14, wadanda akasari ɗalibai ne da ke kan hanyar zuwa rubuta jarabawar JAMB, a jihar Benue.
Lamarin ya faru ne a daren Laraba tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8, lokacin da suka yi wa motar haya da daliban ke ciki daga kwanton bauna.
Motar na ɗauke da kusan fasinjoji 16, inda direba da mutum guda kaɗai suka samu tsira.
Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ce an tura jami’an tsaro domin ceto daliban.
Ita ma rundunar ‘yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kwamishina Ifeanyi Enemari ya ce yana jagorantar aikin ceto domin kubutar da waɗanda aka sace.