Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE ta sanar da cewa ta rusa wata ƙungiyar da ake zargi da ta’addanci mai alaƙa da Iran, wadda ake zargin tana shirin aiwatar da ayyukan ɓarna a cikin ƙasar.
Hukumar Tsaron Ƙasa ta UAE ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta cewa ta kama wasu mambobin wannan ƙungiya, waɗanda ake zargi da ƙoƙarin “lalata haɗin kai da zaman lafiya” a ƙasar.
Hukumar ta ƙara da cewa wannan ƙungiyar da ake kira ta’addanci na ƙoƙarin jawo hankalin matasa domin shiga cikinta, tare da shirya ayyukan ɓarna cikin tsari a cikin iyakokin ƙasar.
Bugu da ƙari, an ce ƙungiyar na tattara kuɗaɗe daga cikin ƙasar sannan tana tura su zuwa ƙasashen waje.