Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan harin jirgin sama da rundunar sojin saman Najeriya ta kai, wanda ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.
Malamin ya bayyana cewa ba a buƙatar ta’aziyya kawai, sai dai a fito da gaskiya da kuma ɗaukar matakin ladabtar da waɗanda ke da hannu a lamarin, yana mai tambayar yadda aka kai hari kan jama’a da basu san komai ba.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya auku ne a wani kasuwa a ƙauyen Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe, inda ake zargin sama da mutane 50 suka rasa rayukansu yayin da ake gudanar da ciniki.
Gumi ya kuma tuna da irin wasu hare-haren da suka faru a baya, yana mai cewa irin waɗannan kura-kurai na soji na ci gaba da janyo asarar rayukan fararen hula, tare da jaddada cewa ba za a iya yaƙar ta’addanci ta hanyar cutar da marasa laifi ba.
A ƙarshe, ya buƙaci Majalisar Dokokin Najeriya musamman Majalisar Dattawa da ta gaggauta gudanar da bincike kan lamarin, domin tabbatar da gaskiya da kuma hana faruwar irin wannan kuskure a nan gaba.